Sakamakon Zaben Shugaban Kasa Na 2023: Jigon APC Ya Ce Peter Obi Ba Zai Yi Nasara A Kotu Ba, Ya Bada

Publish date: 2024-06-07

Jihar Ondo - Kwanaki bayan hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC ta ayyana Bola Tinubu a matsayin zababben shugaban kasa, daya daga cikin abokan karawarsa, Peter Obi, ya yi ikirarin cewa shi ne halattaccen wanda ya lashe zaben 25 ga watan Fabrairu.

Obi ya yi ikirarin cewa shi ya lashe zaben kuma zai tabbatar da nasarar sa a gaban kotu, duk da kasancewar ya yi na uku a zaben. Ya shigar da kara ya na kalubalantar sakamakon zaben.

Kara karanta wannan

Sayen kuri'u: An kori wata karar da ministan Buhari ya shigar kan Tinubu da Atiku

Legit.ng a baya ta kawo jerin da'awa biyar da Peter Obi ya shigar gaban kotun sauraron karrarakin zaben, ciki har da soke zaben Tinubu.

Karar Peter Obi akwai rudani, in ji Jamilu Julius Adebayo

Da ya ke bayani akan lamarin, Jamilu Julius Adebayo, wani jigon APC mazaunin Ondo ya ce Obi ba zai iya nasara a kotu ba.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Ya fadawa Legit.ng:

''Gaba daya karar Peter Obi yaudara ce rudani da addu'ar da ba zata karbu ba. Maganar na'urar BVAS ta watsa sakamakon zabe da zarar an kammala tuni babbar kotun tarayya ta gama hukunci cewa INEC ce ke da ikon yadda za ta watsa sakamakon zabe.''Ba za ka iya ikirarin cewa ka ci zabe bayan ka zo na uku; ka ce BVAS ba ta watsa sakamakon zabe ba, amma a haka kana ikirarin cewa ka ci zabe ta hanyar ita wannan BVAS din dai.''

Kara karanta wannan

To fah: Mataimakin shugaban APC ya fadi yankin da ya kamata a ba kujerar Ahmad Lawal

Ko shari'ar Atiku ta na da madogara?

A gefe guda, Adebayo ya yi sharhi kan yiwuwar dan takarar jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar, ya yi nasara a kotun. Tsohon mataimakin shugaban kasa ya yi na biyu a zaben.

''Kotu za ta yanke hukunci ko ya na da hujjoji da za su sa a soke zabe ko a bayyana shi a matsayin wanda ya yi nasara.''A iya sani na, wannan shi ne zabe mafi inganci a tarihi tun 1999 saboda ya baiwa yan kasa damar zabar wanda ransu ya ke so sabanin bambancin al'ada da addini,'' in ji shi.

Obi ya hadu da Olusegun Obasanjo a filin tashin jiragen sama na Anambra

A wani rahoton, kun ji cewa Peter Obi, dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar Labour a zaben ranar 25 ga watan Fabrairun 2023, ya hadu da Olusegun Obasanjo, tsohon shugaban kasar Najeriya a garin Awka, babban birnin jihar Anambra.

Kara karanta wannan

2023: An Kai Karar Hadimin Tinubu a Babban Kotun Duniya Saboda Bakaken Kalamai

Asali: Legit.ng

ncG1vNJzZmigkarAonrLnp6irF6jtHC6xLCqaGllZ4VygpFmqpqjkaKurLvNZrGampWjerS01KCYm5meYriiv8BmpZplYmV%2FdHnJop6opl2WvaR52JpknJ1dpbK1sdFmppuhXZeubsbAomSyoV2jrrSt0ZpkmmWbpMG2ecGaZLKZXZeupa2MnZiloZyefA%3D%3D